Connect with us

Labarai

Zan buɗe iyakokin Najeriya idan aka zaɓe ni a 2027 -Atiku Abubakar

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya ce zai sake buɗe iyakokin ƙasar nan da ƙasashen makwabta idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

 

Atiku ya ce rufe iyakokin ya yi matuƙar shafar harkokin tattalin arziki a jihohin Arewa da ke makwabtaka da Kamaru, Chadi, Nijar da Benin.

 

Ya ce matasa da dama da ke dogaro da halastaccen kasuwancin ketare sun shiga matsananciyar wahalar kuɗi sakamakon takunkumin da aka sanya.

Ya ƙara da cewa sake buɗe iyakokin zai taimaka wajen farfaɗo da kasuwancin ketare tare da dawo da damar samun sana’o’i da kuɗaɗen shiga ga al’ummomin da abin ya shafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!