Connect with us

Labarai

Najib Hamza ya janye daga takarar Sanatan Kano ta tsakiya

Published

on

Ɗan takarar kujerar majalisar Sanatan Kano ta tsakiya na Jam’iyyar PRP a zaɓen shekerar 2027 da ke tafe Alhaji Najib Hamza, ya sanar da janyewa daga takarar, inda ya shaida cewa ya fasa yin takarar ne saboda wasu dalilai na ƙashin kansa.

 

Alhaji Najib Hamza, ya bayyana janyewa daga takarar ne yayin ganawarsa da manema labarai yau Alhamis a nan Kano.

 

Ya ce, ya janye daga takarar ne bisa ra’ayin ƙashin ƙansa inda kuma ya bai wa magoya bayan jam’iyyar ta PRP haƙuri bisa matakin da ya ɗauka.

 

Ya ce, “Ko kaɗan ban ƙulla wata yarjejeniya da gabanin wannan shiri nawa ba, kawai dai na yi haka ne bisa ra’ayina, kuma za mu jira nan da ɗan wani lokaci domin ganin mataki na gaba da za mu ɗauka.”

 

Haka kuma, ya tabbatar da cewa babu wata alaƙa da ya ƙulla da wani ko kuma wata jam’iyyar kan batun janyewar tasa ya na mai cewa zai ci gaba da kasancewa mamba a PRP ta re da ci gaba da kula da mambobinta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!