Labarai
Har yanzu jihar Kano na mataki na 7 a jihohin da aka fi shaye-shayen kwayoyin maye – NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa ta cafke mutane 60 cikin kwanaki biyu da laifin tu’ammali da kwayoyin maye.
Hukumar reshen jihar Kano ta bakin shugaban hukumar Isah Likita ne ya tabbatar da hakan.
Ya ce “jami’an mu sun kama mutanen ne a guraren shan kayan maye, inda aka same su dumu-dumu suna sha kuna suna buguwa”.
Isah Likita ya kuma ce, hukumar ta samu bayanan sirri ta hanyar raba lambar waya ga al’umma.
“Abinda shugaban hukumar NDLEA ta kasa Janar Buba Marwa mai ritaya ke nufi, na cewa Kano ita ce ta farko da tafi kowace jiha tu’amali da miyagun ƙwayoyi shi ne, jihar ita ce tafi kowacce jiha yawan al’umma dalilin kenan da ya sa ake kallon masu sha suna da yawa.
Likita ya ƙara da cewa, jihar Kano har yanzu tana mataki na bakwai na masu shan ƙwayoyi.
You must be logged in to post a comment Login