Labarai
Har yanzu mata na fuskantar cin zarafi- Barrista Hussaina Aliyu
Tsohuwar shugabar Kungiyar Lauyoyi mata ta kasa reshen jihar Kano Barrista Hussaina Aliyu tace har yanzu mata na cigaba da fuskantar matsalar cin zarafi a wajen maza wanda matsalar ke shafar su har a bangaren siyasa idan sun tsaya takara a siyasa.
Barrista Husaina Aliyu ta bayyana haka ne ta cikin shirin muleka mu gano na musamman na gidan Radio Freedom daya mayarda hankali kan bikin ranar mata ta duniya da majalisar dinkin duniya ta ware ranar sha uku ga watan Maris.
Husaina Aliyu Ibrahim tace abun takaicin ma ba iya nan matsalar ciwa mata zarafi ta tsaya ba harda cigaba da kiran sunan mace da wani suna mara dadin ji da maza keyi idan sun tsayawa takara ta siyasa a kowacce jam’iyya wanda hakan ke sanya rayuwar mata cikin damuwa.
Barista Husaina Aliyu Ibrahim ta nanata cewa mata a yanzu na fuskantar matsala musamman a bangaren zamantakewar su ta aure a wajen mazajen su wanda a yanzu matsalar ke cigaba da samun gindin zama a tsakanin su.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa daya bibiyi yadda shirin ya gudana ya ruwaito Tsohuwar shugabar kungiyar na cewa ko a bangaren daukar aiki ma ana barin mata a baya saka
You must be logged in to post a comment Login