Labarai
Hedikwatar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta kama wani fitaccen dan daba da ake kira Linga tare da abokinsa Guchi.

Hedikwatar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta kama wani fitaccen dan daba da ake kira Linga tare da abokinsa Guchi.
A wata sanarwa da kakakin rundinar ‘yansandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce an kama su ne bayan sun dade suna wallafa bidiyo a shafukan TikTok da Facebook suna nuna makamai tare da tada hankalin jama’a. Jami’an tsaro sun gano takobi da sanduna a hannunsu lokacin da aka kama su a unguwar Dala.
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar ta fara bincike a kansu, tare da gargadin cewa duk wanda ya dauki bidiyo yana nuna makamai ko ya tsunduma cikin ta’addanci za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Rundunar ta kuma yi kira ga iyaye da su ja hankalin ‘ya’yansu kan gujewa harkar ta’addanci. Ta kara da cewa za ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Hedukwatar ta kuma gode wa jama’a bisa bayanan sirri da suke bayarwa, tare da bukatar a ci gaba da bayar da rahoton duk abin da ake zargi ta wayar:
08032419754, 08123821575 da 09029292926.
Hoto: SP Abdullahi Haruna Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login