Labarai
Hisbah ta ƙulla yarjejeniya da ƴan kasuwar Kwanar Gafan
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ƙulla yarjejeniya da ƴan kasuwar Gwari ta kwanar Gafan dake ƙaramar hukumar Garin Malam a nan Kano.
Hisbar ta ƙulla yarjejeniya da ƴan kasuwar ne domin yin aiki tare da jami’an ta wajen tabbatar da bin dokokin shari’a tare da kaucewa aikata baɗala.
A cikin wata sanarwa da mai taimakawa babban kwamandan Hisbah na jiha Bashir Muhammad Sani ya fitar a yau Lahadi ta ce, an ƙulla yarjejeniyar ne a yayin wata ziyara da tawagar hukumar ta kai kasuwar a yau.
Sanarwar ta ce, jami’an Hisbah bisa jagorancin babban kwamandan Malam Muhammad Harun Ibn Sina sun gana da shugabannin kasuwar inda suka tattauna batutuwa da dama tare da tunasar da ƴan kasuwar kan su ci gaba da yin kasuwanci tare da riƙo da gaskiya da kuma kyawawan halaye da addinin musulunci ya koyar.
Idan zaku iya tunawa dai tun a shekarun baya an sha kai ruwa rana tsakanin ƴan kasuwar da jami’an hukumar Hisbah kafin samun wannan yarjejeniya, domin ko a shekara ta 2012 an samu mummunan rikici wanda yayi sanadiyar raunata ƴan Hisbah sama da 40, inda su kuma ƴan Hisbah suka cafke mata masu zaman kan su sama da 89 a kasuwar.
Hotuna a yayin ziyarar.
You must be logged in to post a comment Login