Labarai
Hisbah ta yi kame a Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sha alwashin ci gaba da yaƙar masu aikata baɗala a lungu da saƙo na jihar Kano.
Babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina, shi ne ya bayyana hakan a yau Talata, lokacin da hukumar Hisbah ke holen matasan da ta kama a unguwannin Ɗorayi da Ja’en da kuma Janguza, a sakamakon rahoton sirri da mazauna unguwanin suka bai wa hukumar ta Hisbah, na aikata abubuwan da basu dace ba.
A nasa ɓangaren babban daraktan hukumar Hisbah, Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya ya ja kunnen matasan da su ƙara jin tsoron Allah domin mutuwa ka iya riskar mutum a kowane lokaci.
Daga cikin matasan da Hisbah ta yi holen su akwai samari da ƴan mata masu shekara 14 zuwa sama, waɗanda suka zo Kano da sunan aikatau.
A ƙarshe hukumar Hisbah ta ce zata aika da matasan zuwa gaban kotu domin yanke musu hukunci kan laifukan da ake zargin su da aikatawa.
You must be logged in to post a comment Login