Labarai
Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da sabbin kudaden aikin Hajjin 2027

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da sabbin kudaden aikin Hajjin 2027 da gwamnatin ta da su, bisa la’akari da farashin ayyuka, canjin kudin waje da jin dadin mahajjatan.
Kudin Hajjin ya bambanta bisa yankunan da kowane Mahajjaci zai tashi, inda mahajjatan Maiduguri da Yola za su biya N7,560,822, na yankin Arewa N7,672,822, yayin da na yankin Kudu za su biya N7,882,822.
NAHCON ta ce wadanda suka riga suka biya N5,000,000 za su biya ragowar kudin domin kammala rajistarsu, yayin da sababbin masu rajista za su biya ta hukumomin jin dadin Mahajjata na jihohinsu ko bankunan da ke cikin tsarin ajiyar kudin Hajji.
Hukumar ta sanya 26 ga Satumba 2026 a matsayin wa’adin karshe na shigar da bayanan biometric na mahajjata cikin manhajar Nusuk-Masar, yayin da jihohi za su kammala tura kudaden Hajjin zuwa 2 ga Disamba 2026. NAHCON ta gargadi cewa ba za a kara wa’adin ba, kuma kasa cika sharuddan na iya janyo asarar guraben Hajjin da aka ware.
You must be logged in to post a comment Login