Labarai
NAHCON ta sake jaddada ranar kammala rajista da biyan kuɗin aikin Hajjin badi

Hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON, ta sake tunatar da maniyyatan Hajjin 2027 cewa ranar 26 ga Satumba ce wa’adin kammala rajista da biyan kuɗin aikin Hajjin.
Hukumar ta yi wannan tunatar wa ne a wasu saƙonni da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, inda ta buƙaci maniyyatan da ba su kammala rajista da biyan kuɗaɗen ba da su yi hakan kafin cikar wa’adin.
NAHCON ta ce wa’adin shi ne jadawalin da hukumomin Saudiyya suka bayar domin shirye-shiryen aikin Hajjin 2027.
Hukumar ta ce kammala wannan aiki cikin lokaci ya zama wajibi domin daidaita bayanan maniyyata da kuma rabon kujerun jirgi, tana mai gargaɗin cewa rashin cika wa’adin na iya janyo rasa guraben Hajjin da aka ware wa maniyyata.
A watan Agusta, NAHCON ta sanar da kuɗin aikin Hajjin 2027, inda maniyyatan da za su tashi daga Maiduguri da Yola za su biya N7,560,822, yayin da na yankin Arewa za su biya N7,672,822.
Maniyyatan yankin Kudu kuwa za su biya N7,882,822.
You must be logged in to post a comment Login