Labarai
Yan sanda a jihar Kebbi za su cafke ababen hawa masu baƙin gilashi da rufe lambobi ba bisa ka’ida ba

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta ce za ta ci gaba da aiwatar da Operation Velvet domin cafke ababen hawa masu bakin gilashi da basu da shaidar izini da waɗanda aka rufe lambobinsu.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar a ranar Alhamis 13 ga Agusta 2026.
Ya ce, Rundunar za ta sake dawo da aikin a ranar Juma’a 14 ga Agusta 2026, inda za a tabbatar da bin dokokin hanya, rajistar ababen hawa da sauran laifukan zirga zirgar ababen hawa.
Sanarwar ta ce, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Umar M. Hadejia, ya ce matakin zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan tsaro.
Rundunar ta umarci jami’an da za su gudanar da aikin su kasance masu ƙwarewa da ladabi, tare da mutunta haƙƙin jama’a.
You must be logged in to post a comment Login