Labarai
NDLEA ta cafke tarin miyagun kwayoyi da aka boye a kayayyakin da aka shigo da su

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta ce ta cafke wasu tarin miyagun kwayoyi, wadanda aka boye a cikin kayayyakin da aka shigo da su Najeriya, a samamen da ta gudanar a wasu jihohin kasar nan.
Haka kuma, an gano wasu tarin miyagun kwayoyi guda biyu da aka boye a cikin lasifikokin kiɗa, inda aka cafke su a wasu tashoshin mota a Jihar Legas.
A cewar kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, akalla mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen safarar miyagun kwayoyin, da jami’an hukumar suka kama a yayin samamen.
A wani samame da jami’an NDLEA suka gudanar a sashen ajiyar kayayyakin da ake shigowa da su kasar nan , na filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Lagos, jami’an sun gano wani kaya da ake shirin aikawa zuwa Birtaniya.
You must be logged in to post a comment Login