Labarai
Kano: Ƴan sanda sun kama mutane 248 da ake zargi da manyan laifuka

Rundunar ƴan Sandan jihar Kano, ta ce, ta kama mutane 248 da ake zargi da hannu a aikata laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, safarar miyagun kwayoyi da kuma tayar da tarzoma cikin wata guda.
Kwamishinan ƴan Sandan jiha Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai a nan Kano.
Ibrahim Adamu Bakori ya ce, daga cikin wadanda aka kama akwai mutane 18 da ake zargi da fashi da makami, biyar masu garkuwa da mutane, 32 masu safarar miyagun kwayoyi, 12 masu satar motoci, 11 masu satar adaidaita sahu, shida masu satar babura da kuma wasu 15 da ake zargi da sata.
Ya kara da cewa, an kama mutane 149 da ake zargi da hannu a rikice-rikicen tarzoma da suka faru a sassa daban-daban na jihar
Rundunar ta ce ta kwato makamai masu hadari da dama da suka hada da bindiga kirar pistol guda daya, bindigogi da kera a gida guda hudu,da harsasai guda biyar da kuma addina guda 232 sai wukake 374 da gatari 13 kibiyoyi 23 da gororo 37 da sauran su
Haka kuma, kwamishinan ya buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da bayanan sirri.
You must be logged in to post a comment Login