Labarai
Hukumar EFCC za ta fara gurfanar da Angwaye a Kotu
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu ya bayyana cewa, hukumar za ta kama duk wasu Ango da Amarya da aka yi watsin kudi a wajen shagalin bikinsu.
Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Makurdin jihar Benue.
Ya ce, mutane na amfani da kudaden Najeriya da kasashen ketare wajen yi wa angwaye liki da su wanda hakan ya ci karo da dokar kasa.
Ibrahim Magu ya kara da cewa, daga yanzu za ta fara hana tariyar duk wadanda ta kama ana watsi da kudin da suka wuce kima a bikinsu ta hanyar gabatar das u a gaban kotu.
Shugaban hukumar ta EFCC ya kara da cewa, ko a kwanakin baya sai da hukumar ta ja kunnen wasu daga cikin ‘yan siyasa kan yadda suke watsi da kudade a wuraren biki tare da yin shigar kece raini da kuma nuna dukiya hanyar fito da gwalagwalai da makamantansu.
Ya kuma kara da cewa, yanzu haka hukumar tasa ta samu nasarar hana ‘yan siyasar da ke da irin wannan hali na halartar tarukan kece raini a cikin kasar nan har ma da kasashen ketare.