Labarai
Hukumar Gyaran Hali ta Kano ta ce sauya Abduljabar zuwa kuje na daga cikin ka’idojin aiki

Hukumar lura da gidan Ajiya da gyaran Hali na Kasa reshen Jihar Kano ta ce canjin da akayiwa Malam Abduljabar Nasiru Kabara daga Gidan Ajiya da Gyaran Hali na Kurmawa zuwa babban Gidan Ajiya da Gyaran hali na Kuje ba wani sabon abu bane, da hakan na da nasaba cika ka’idojin aiki.
Mai magana da yawun hukumar reshen Jihar Kano CSC Musbahu Kofar Nassarwa ne ya bayyana hakan a wata murya da ya aikewa Freedom Radio.
CSC Musbahu Kofar Nassarwa ya ce ba Malam Abduljabar Nasiru Kabara kadai canjin da akayi ya shafa ba, harda wasu mazauna gidan Ajiya da Gyaran Hali zuwa Kuje.
You must be logged in to post a comment Login