Labaran Kano
Hukumar Hisbah ta Kano ta cimma yarjejeniyar aiki da KAROTA
Hukumar Hisbah ta jihar Kano da na KAROTA sun kammala cimma yarjejeniyar hada hannu don tabbatar da cewa masu ababan haw ana bin ka’idojin hanya bda toki a ciki da wajen birnin Kano.
Babban kwamnadan hukumar ta Hisba Sheik Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar aiki ga babban manajan daraktan hukumar ta KAROTA Alhaji Baffa Babba Dan Agundi a offishin sa.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na Hukummar Hisba Lawan Ibrahim Fagge ya fitar cewa, shugaban hukumar ta Hisbah Harun Ibini Sina suna da nasaba ta aiki da na KAROTA Baffa Babba Dan Agundi wajen tabbatar da zaman lafiya da bin ka’idojojin aiki ta hanyar kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Kano baki daya.
Hukumar Hisbah ta gana da saurayin dake shirin auren Ba’amurkiya
Hisbah zata bude sabbin ofisoshi a Kano
Da dumi-dumi: Hisbah ta janye dokar hana cakuda maza da mata
Da yake jawabi shugaban na KAROTA Babba Dan Agundi ya bayyana ziyarar da hukumar ta Hisbah ta kawo masa a matsayin abun a yaba, yana mai cewar, nan bada jimawa ba hadin gwiwar zai fara aiki don tabbatar da al’ummar jihar Kano na bin ka’idojojin aiki.
Shugaban na KAROTA ya kuma yabawa masu ababan hawa da matoka wajen marawa hukumar ta KAROTA baya.