Kiwon Lafiya
Hukumar INEC ta dakatar da jami’an ta 205 da aikata wasu laifuka
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da wasu jami’an ta 205, sakamakon aikata laifuka daban-daban yayin zaben shekarar 2015.
Shugaban hukumar na kasa farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi yayin taron wani kwamitin mai zaman kan sa da ke sanya ido kan yadda ake gudanar da ayyuka da aka gudanar a Abuja.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa hanawa da nadawa, hadi da karin girma da kuma tsawatarwa da hukumar take aiwatarwa ya kai matakin da ake bukata.
Farfesa Mahmud Yakubu ya kara da cewa irin korafin da hukumar take samu daga al’ummar kasar nan, ya taimaka mata wajen cimma manufofi da dama, musamman ma wajen tabbatar da sahihancin zabe.
Yace yanzu haka hukumar na cigaba da gudanar da ayyukan tunkarar babban zaben shekarar 2019, tare da cewa akwai bukatar hukumar ta zabo gogaggun ma’aikatan da zasu yi mata aikin zaben na shekarar badi.