Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar INEC ta fara daukar ma’aikatan wucin gadi gabanin fara baban zabe

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fara daukar ma’aikatan wucin gadi gabanin fara babban zabe da za’a yi ranar 16 ga watan Fabareru.

Wannan na kunshi cikin sanarwar da hukumar ta fitar a shafin ta na Twitter cewa zata dauki ma’aikatan wucin gadi da ya kama daga jami’an sanya idanu da masu kula da tantance kuri’u da mataimakan baturan zaben da dai sauran su.

 A cewar, sanarwar hukumar ta INEC ta bude shafin ta daga jiya Talata don baiwa masu sha’awar aikin neman aikin, a yayin da zata rufe shafin a ranar  Litinin 21 ga watan nan da muke ciki da misali karfe 8 na safe.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!