Kiwon Lafiya
Hukumar INEC ta gano hanyar da wasu baragurbi yan siyasa ke amfani da shi wajen sayen kuri’u
Hukumar zabe ta kasa (INEC), ta ce ta gano wasu sabbin hanyoyi da wasu baragurbin ‘yan siyasa su ke son amfani da shi wajen sayan kuri’un jama’a, yayin zaben kasa da za a yi a watan gobe.
Kwamishina a hukumar zabe ta kasa (INEC), Mr. Festus Okoye ne ya bayyana haka lokacin da ya ke ganawa da sarakunan gargajiyar jihar Osun a garin Osogbo.
Mr Festus Okoye wanda ya samu wakilcin kwashinan zabe mai kula da jihar Osun Mr Segun Agbaje, ya ce, sun samu labarin cewa wasu baragurbin ‘yan siyasa suna yaudaran jama’a kan su basu katunan zaben su ko kuma su gaya musu lambobin sirrin da ke jikin katunan zaben.
Ya ce manufar hakan shine hana masu rike da katunan zabe samun damar kada kuri’a a lokacin zabe ko kuma su yi kutse cikin websites din hukumar ta INEC.
Kwamishinan hukumar ta INEC ya kuma ce duk wanda aka kama yana aikata haka to kuwa ya tabbata zai dandana kudarsa.