Kiwon Lafiya
Hukumar INEC ta nesanta kan ta da kalaman gwamnan jihar Kaduna
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta nisanta kan ta da kalaman da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa’I kan cewa duk ‘yan kasashen wajen da suka yayi katsalandan cikin harkokin zaben kasar nan za’a maida gawawakin su kasashen su.
Gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da wani shi na kai tsaye da tashar talabijin ta NTA a shekaranjiya Talata, Yana mai cewar duk wanda yake kiran ‘yan kasashen waje su zo tsoma baki cikin harkokin zaben kasar nan, ‘muna jiran su, babu shaka za’a koma da gwawakin su kasahen su.
A yayin da ake tattaunawa da shi ta cikin wani shiri na gidan talabijin na Channels, kwamishinan zabe na jihar Akwa Ibom Mike Igini ya ce masu sanya idanu na kasashen waje da kasa su firgita kuma gwamnan na Kaduna ya bayyana ra’ayin sa ne, ba wai ra’ayin hukumar ta INEC bane. A don haka ya ce, Mike Igini ya kara da cewar, masu sanya idanu na kasashen waje su kwana da shirin cewar Nasiru El-rufa’I baya yana Magana da yawon hukumar bane, kuma hukumar na tare da su dari bisa dair.