Labarai
Hukumar jiragen kasa ta kasa ta nemi afuwan fasinjoji
Hukumar jiragen kasa ta kasa ta bayyana damuwarta da rashin jin dadin ta sakamakon rashin tashi da jirgin yayi a ranar talatar da ta gabata kamar yadda aka tsara wanda zai dauki fasinja daga Abuja zuwa Kaduna.
Mataimakin daraktar sashin yada labarai Mal Yakub Moahmood ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya ga kamfanin dillancin labarai.
Ya ce hukumar ta bayyana rashin jin dadinta na rashin aiki da jirgin yayi a ranar talatar da ta wuce, inda aka samu matsala daga tashar ta Rigasa dake jihar Kaduna.
Katsina:wani jirgin shalkwabta rundanar sojin kasar nan yayi hadari
Farfelar jirgin saman rundanar sojin kasar nan ya fille kan want hafsan sojin sama
Najeriya ta rasa yan kasar ta guda biyu a hatsarin jirgin saman kasar Ethopia
Hukumar ta nemi afuwa dukkanin fasinjojin na faruwar hakan, tare da neman afuwarsu.
Mahmood ya kara da cewa tuni aka magance matsala kuma jiragen suka fara aiki yadda ya kamata