Labarai
Hukumar KAROTA ta cafke miyagun kwayoyi a Kano
Hukumar lura da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta gano wasu miyagun kwayoyi da kudinsu ya tasamma miliyan 25 a yankin unguwar Sabon Gari.
Kwayoyin wadanda suka kunshi masu karawa maza karfin mazantaka mai suna Arofranil an gano su ne bayan wani binciken da aka tabbatar basa dauke da lambar hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC.
An dai gano jabun magungunan ne makare a wata motar dakon kaya a yankin na Sabon Gari da ke kwaryar birnin Kano ana kokarin rarrabawa ga masu hada-hadar magunguna.
Sinki dubu biyar na maganin jami’an hukumar NAFDAC din suka kama yayinda ake binciken masu kayan, ko da yake hukumomin da abun ya shafa tuni suka fara farautar su a halin yanzu.
Karin labarai:
Covid-19: KAROTA ta gargadi masu shirin taron daurin aure
KAROTA ta kama babbar mota makare da giya
Hukumar KAROTA ta ce zata mika magungunan ga kwamitin kar-ta kwana kan jabun magunguna na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano. Domin daukar matakan da suka dace.
Wannan na kunshe a wata sanarwa da hukumar KAROTA ta fitar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a Nabilusi Abubakar K/Na’isa.
Sanarwar ta ruwaito shugaban hukumar ta KAROTA Baffa Babba Dan’agundi na kira ga al’ummar Kano da su bawa hukumar goyon baya wajen kakkabo bata garin da ke neman kawo tarnaki wajen ciyar da jihar Kano gaba.
You must be logged in to post a comment Login