Labarai
Hukumar KAROTA ta kama Direban da ya kade jami’inta

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano Karota ta samu nasarar kama Direban daya kade jami’in ta mai suna Nasiru Abdullahi a sashin su dake Danbatta wanda ya yi sanadiyyar samun raunika a jikinsa.
Mai magana da yawun hukumar Malam Abubakar Ibrahim Sharada, ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aiko wa Freedom Radiyo.
Ya kara de cewa, za su gurfanar da mutumin a gaban kotu domin girbar abin da ya aikata.
You must be logged in to post a comment Login