Labarai
NAWOJ ta taya Correspondent Chapel murnar kammala gyaran ofishinta

Ƙungiyar ƴan Jarida mata ta Najeriya reshen jihar Kano NAWOJ, ta taya ƙungiyar ƴan jarida masu aikewa da labarai reshen jihar kano murnar kammala gyaran ofishinsu, ƙarƙashin jagorancin Kwamared Murtala Adewale.
NAWOJ Kano ta yaba da ƙoƙarin shugabancin bisa inganta yanayin aiki da samar da kyakkyawan muhalli ga ‘yan jarida, domin kara bunkasa kwarewa da aikin jarida.
Shugabar ƙungiyar Sayyada Bahijja malam Kabara ce, ta bayyana hakan a wani sakon murya da ta aiko wa Freedom Radio ta hannun mataimakiyar Sakariyar kungiyar Kwamrade Aisha Muhammad Yalleman.
Ƙungiyar ta bayyana gyaran ofishin a matsayin wani abin a yaba, wanda zai samar da yanayi mai kyau da jin dadi ga ‘yan jarida wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login