Labarai
Mun ta fara yin amfani da fasahar zamani wajen tsaron iyakokin Najeriya- NIS

Hukumar kula da shige da fice NIS, ta ce ta fara yin amfani da fasahar zamani wajen tsaron iyakokin Najeriya.
Kwanturola Janar ta hukumar, Kemi Nandap, ce ta bayyana hakan a jihar Lagos, yayin wani taro na jami’an da ke kula da iyakokin kasashen Afrika.
Ta ce, hukumar na amfani da tsarin tantance shaidar mutum ta zamani, da na’urorin sarrafa zirga-zirgar mutane ta atomatik da kuma sa ido bisa bayanan sirri, domin karfafa tsaron iyakoki ba tare da hana halastacciyar zirga-zirga da cinikayyar kasashen ketare ba.
Kemi Nandap ta ce ya kamata a daina kallon tsaron da ake baiwa iyakokin kasashe a matsayin hanyar raba kan kasashe.
A cewarta, babban kalubalen gwamnati shi ne tabbatar da tsaron iyakoki tare da tabbatar da cewa matafiya, ‘yan kasuwa da al’ummomin da ke zaune a kan iyakoki ba su fuskanci takura ba.
You must be logged in to post a comment Login