Labarai
Hukumar kula da al’amuran ‘yan sanda zata bibiyi hallayar jami’anta
Hukumar dake kula da al’amuran ‘yan sanda ta kasa, ta ce zata bibiyi hallayyar da jami’an ‘yan sanda za su gudanar a yayin babban zaben wannan shekarar, don gano ko sun yi amfani da kwarewar su.
Kwamishiniyar ‘yan sanda Hajiya Najatu Muhammad ta bayyana hakan a yayin taro da manema labarai a birnin Dutsen jihar Jigawa cewa makasudun bijiru da wannan matakin shine don tabbatar da an gudanar da zaben cikin gaskiya.
Hajiya Naja’atu ta ce a yayin da zaben ke karatowa akwai bukatar a janyo hankalin al’umma da masu ruwa da tsaki kan muhimmancin da babban zaben ke da shi ga kuma jami’an ‘yan sanda.
Akan haka ne hukumar dake kukla da lamuran ‘yan sanda ta kasa ta maida hankali kan dabiun jami’an ta a zaben dake tafe kasancewar hukumar na da kashi 85 cikin 100 na jami’an tsaro a fadin kasar nan.