Kiwon Lafiya
Hukumar kula da kamfanoni sadarwa ta ce ta gano yadda ake cirewa kwastamomi kudade babu gaira babu dalili
Hukumar dake kula da kamfanonin sadarwa ta kasa NCC ta sanar da cewa, ta gano yadda kamfanonin sadarwa ke cirewa kwastomomi kudade a layukan su na wayoyi babu-gaira-babu-sabar.
Hukumar ta NCC ta sanar da hakan ne a cikin shafin ta na Internet cewa, nan bada jimawa ba ne, zata baiwa kamfanonin sadarwar umarnin mai da kudaden da ta cire na kwastamomi ba tare da sahalewar su ba.
Haka zalika hukumar dake kula da sadarwa ta kasa ta ce, ta gano hakan ne, bayan da ta karbe korafe-korafen jama’a kan ana cire musu kudaden idan sun sanya kudi cikin layukan su, yayin da hukumar ta kaddamar da bincike kan batun. Sashin dake bibiyar ayyuka da bin dokoki na hukumar ta NCC ya bayyana cewar, hukumar ta aike da ayarin masu bincike don faiyace batun, bayan hakan ne sai hukumar ta bayar da layukan waya don tuntubar ta