Connect with us

Labaran Wasanni

Covid-19: An dakatar da kwallon kafa a Kano saboda Coronavirus

Published

on

Tun bayan sanarwar da hukumar Kwallon kafa ta Kasa (NFF) ta fitar na dakatar da dukkan wasannin Kwallon kafa a kasar nan, sakamakon cutar Coronavirus, kungiyoyin Kwallon kafa a jihohin kasar nan, na bin umarnin sau da kafa, ciki har da hukumar Kwallon kafa ta jihar Kano.

A wata sanarwa, da sakataren hukumar ta jihar Kano Alhaji Shehu Buhari ya sakawa hannu, ta umarci dukkanin hukumomin Kwallon kafa na kananan hukumomin jihar 44, da su dakatar da komai ba gudanar da wasanni har zuwa abinda hali ya yi na yadda aka tunkari cutar ta Corona ko kuma shawo kan yaduwar ta.

Jim kadan, bayan fitar da sanarwar, kungiyoyi da dama da suka hadar da Kano Pillars, ta bakin kakakin ta Rilwanu Idris Malikawa, ta sanar da bin dokar sau da kafa tare da umartar ‘yan wasan kungiyar da su tafi hutu.

Haka ita ma kungiyar Kwallon kafa ta Ramcy Fc, dake gidan Sarki, ta bada umarnin bin dokar tare da tsaida atisaye da tura ‘yan wasanta hutu zuwa abinda hali ya yiwu, a ta bakin jami’in yada labaranta Aminu Abba Kwaru.

Karin labarai:

Kano Pillars ta lallasa Jigawa Golden Stars

Kano Pillars ta lallasa Delta Force da ci 6-1

A bangare daya, kuma hukumar Kwallon kafa ta Tarauni, ta bakin Sakataren ta Isma’il Fango, da kakakin ta Rufa’i Bateza Unguwa uku, sun sanar da dakatar da komai da ya shafi Kwallon kafa a karamar hukumar har sai an ga yadda ta yiwu dangane da barazanar cutar ta Covid-19.

Zuwa yanzu dai a iya cewa, harkokin Kwallon kafa a fadin jihar Kano, birni da kauyuka sun tsaya cik, sakamakon bin umarnin hukumar Kwallon kafa ta jiha karkashin jagorancin Sharif Rabiu Inuwa Ahlan, wadda ita ma ta karbi umarnin dakatarwar daga hukumar Kwallon kafa ta Kasa karkashin Mista Amaju Melvin Pinnick.

A ‘yan kwanakin nan, harkokin Kwallon kafa a duniya ya samu tsaiko, sakamakon bullar cutar ta Corona Virus, dake kara yaduwa a fadin duniya, inda manyan kasashe masu dumbin magoya baya da kuma manyan kungiyo dake taka Leda, da suka hada da Italiya, Faransa, Jamus(Germany ) Andalus(Spain) da kasar Ingila suka dage wasannin gasar kakar kasashen su bisa bullar cutar a kasashen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

NMA: Rashin tsaftar muhalli na kawo yaduwar cutar Covid-19

Published

on

Kungiyar likitoci ta kasa reshan jahar kano NMA ta bayyana cewar rashin tsaftar muhalli a tsakanin al’umma ke kara yaduwar cutar corana da ake fama da ita a fadin Duniya.

Shugaban kungiyar Dakta Sanusi Muhammad Bala ne ya bayyna hakan jim kadan bayan kammala shirinn barka da hantsi na nan tashar freedom radiyo.

Ya kuma ce akwai bukatar al’umma su kara kula da tsaftar muhalin su da jikin su dan kaucewa kamuwa da cutuka.

Covid-19: Kungiyar likitoci NMA ta raba kayan kare kai

Covid-19: NMA ta bukaci membobinta da suka tsindima yajin aiki da su dawo aiki

Dakta Sanusi Muhammad ya kuma kara da cewar akwai bukatar samar da dakunan kwaje-kwaje a nan Kano domin ganin an inganta harkar lafiya duba da halin da ake ciki duk da cewar gwamnatin tarraya ta bada umarnin samar da dakunan gwajin a wasu jahohi.

Ana sa bangaran Khalid Sanusi Kani dalibi mai karantar fannin likata a Jami’ar Bayaro dake nan kano bayyana cewa yai a matsayin su na dalibai za su gudanar da tsare-tsare don kara wayar da kan al’umma game da cutar ta corona duba da cewar har yanzu akwai wanda basu yadda da ita ba.

Bakin sun kuma yi kira ga jama’a su kasance masu bin sawarwarin likitoci dan ganin an kaucewa kamuwar cutar ta Corona.

Continue Reading

Labaran Wasanni

Tsohon Kocin Atletico Madrid ya mutu

Published

on

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid da Barcelona da Real Madrid, Radomir Antic, ya mutu  hakan ya biyo bayan rasuwar mahaifiyar mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Joseph Gurdiola wadda ita ma ta rasu a jiya bayan fama da cutar Corona.

Radomir Antic ya rasu yana da shekaru 71, bayan gajeruwar rashin lafiya da bata da alaka da cutar Corona, wadda ake fama da ita a halin yanzu a fadin duniya.

Antic wanda ya  shafe shekaru 27, yana horar da kungiyoyi daban -daban ya yi kaurin suna ne a kungiyar Atletico Madrid, wacce ya jagoranta wajen lashe gasar  LA liga, da kofin kalubale a kasar wato Copa Del Rey a shekarar 1995-96, kafin daga bisani ya rike kungiyoyin Barcelona da Real Madrid.

Labarai masu alaka.

Yanzu-yanzu: Dan wasan kungiyar Enugu Rangers ya Mutu

Muller ya saka hannu a sabon kwantiragi da Bayern Munich

Tuni dai shugaban kungiyar Atletico Madrid, Miguel Angel Gil, ya nuna alhinin sa tare da mika ta’aziyyar sa ga iyalin mamacin tare da cewar an yi rashin gwarzon hazikin jagora, in da kungiyoyin Madrid da Barcelona, suma suka aike da sakon  ta’aziyyar su.

Radomir Antic, dan kasar Serbia, ya rike kungiyoyi da dama ciki har da kasar sa ta haihuwa, da suka hada da , Real Zaragoza, Celta Vigo, Real Oviedo, kafin ya karbi aiki a  Barcelona a shekarar 2003 da ya canji Luis Van Gaal, ya karkare a kungiyar Hebei China Fortune, a kasar China,a shekarar 2015.

 

Continue Reading

Labaran Wasanni

Muller ya saka hannu a sabon kwantiragi da Bayern Munich

Published

on

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich Thomas Muller, ya sake sabunta yarjejeniyar kwantiragin cigaba da wakiltar kungiyar na shekaru uku zuwa shekarar 2023.

Mai shekaru 30, Muller wanda ya fara wakiltar kungiyar ta Bayern a shekarar  2008, ya kara kwantiragin nasa da zai tsawaita shekarun sa  da za su haura shekar 15, yanzu haka da ya shafe a kungiyar.

A baya dai dan wasan, ya nuna aniyar sa ta shirin barin kungiyar a watan Janairu,  wanda hakan ya kawo rade radin  na cewar zaman  dan wasa a kungiyar ya kare, da kungiyoyi irin su Totenham, Manchester United da Juventus da Inter Milan, suka nuna sha’a war daukar dan wasa.

Sai dai yanzu haka saka hannu akan kwantiragin da dan wasan ya yi, ya kawo  karshen rade radin da ake na barin sa kungiyar, wanda a yanzu haka dan wasan ya buga wasa sama da 500, ga kungiyar ta Bayern, ya kuma zura kwallo goma a gasar kakar wasa ta bana kafin ta samu tsaiko da bada taimako wajen zura kwallo sau 18.

Labarai masu alaka.

Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni

Yadda wasannin zakarun nahiyar Turai ke gudana

Shugaban kungiyar ta Bayern Munich, Karl Heinz Rummeniegge, da daraktan wasanni Hasan Salihamidizic, sun bayyana jin da din su da yabawa dan wasan da hazakar sa a cikin filin wasa.

Thomas Muller, ya dau kofin duniya  a shekarar 2014 da aka kammala a kasar Brazil, ya kuma lashe gasar champions league a shekara ta 2013, tare daukar gasar Bundesliga ta kasar Jamus, sau takwas da lashe gasar kofin kalubale na kasar mai taken DFB Pokal har sau biyar, sai gasar kungiyoyin nahiyoyi ta world club cup sau daya.

Zuwa yanzu haka dai kungiyar Bayern, ke kan gaba a gasar ta Bundesliga da maki 55, bayan zagayen wasanni 25 inda ta bada tazarar maki hudu ga mai biye mata  kungiyar Dortmund, kafin  a dakatar da gasar sakamakon Corona Virus.

 

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 316,595 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!