Labaran Kano
Hukumar Kwastam ta kama tirelar kayan Naira miliyan dari a Kano
Hukumar hana fasakwauri ta kasa shiyyar jihar Kano da Jigawa ta kama kayan gwanjo, da shinkafa da man girki da kudinsu ya kai kusan Naira miliyan dari a nan Kano.
Kwanturolan Hukumar a nan Kano Nasir Ahmad, ne ya bayyana hakan ga manema labarai da safiyar Yau talata a ofishinsu dake nan Kano.
Nasir Ahmad, ya kuma kara da cewar Hukumar ta kwastam za ta cigaba da zabarin masu fasakwauri don tabbatar da ta dakile shigo da kayan da doka ta hana shigo da su cikin kasar nan, da nufin inganta tattalin arziki, tsaro da kuma bunkasa masana’antun cikin gida.
Ya kara da cewa da taimakon sojoji ne suka kama motar tirela makare da gwanjo daga garin Aba a daidai filin Idi na Kofar Wambai.
Ya kuma ce kayan zasu kai kimanin na miliyan dari da suka hadar da shinkafa da mai da sauransu.
A halin da ake ciki dai an bada bilin wanda aka kama kamar yadda doka a tanada. Ya ce kasancewa doka ta haramta shigo da wadannan kaya hakan ce ta sa aka kama su
Kwantorolan hukumar hana fasakwaurin ya kara da cewar kamata yayi yan kasuwa da sauran masu kishin Kasa su cigaba da bawa hukumar hadin kai wajen dakile ayyukan fasakwauri wanda wasu ke amfani da hakan wajen shigo da kwaya ko makamai.
Ya ce aikine na kowa , ya bukaci yan kasuwa da su daina shigo da kayayyakin da aka haramta , wanda ta haka ne ma ake shigo da kwaya da ma makamai a wasu lokutan.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewar hukumar ta kuma kama baburan Adaidaita Sahu guda uku da ake amfani dasu wajen safarar shinkafa a nan Kano.