Labaran Wasanni
Hukumar NBBF za ta cigaba da gudanar da gasar kwallon Kwando duk da kai ta kara da aka yi
Hukumar kwallon Kwando ta kasa NBBF ta ce, za ta ci gaba da gudanar da gasar kwallon Kwando ta Maza kamar yadda aka tsara, duk da cewa wasu kungiyoyi biyu sun kai hukumar kara gaban kotu.
Kungiyar kwallon Kwando ta Gombe Bull da Kwara Falcons da suka buga wasan karshe na gasar bana, su ne suka shigar da karar don kalulabantar bangaren shugabancin hukumar na Tijjani Umar, wanda ya shirya gasar, kasancewar su ya kamata su wakilci kasar nan a gasar kwallon Kwando ta Afrika.
Sai dai shugabancin hukumar bangaren Musa Kida ya ce, bai yarda da tsarin ba inda ya ce zai shirya wata gasar wadda za ta gudana tsakanin ranakun 13 zuwa 17 ga watan Nuwambar nan da muke ciki, kuma wadanda suka samu damar zuwa wasan karshe ne za su wakilci Najeriya a gasar kwallon Kwando ta Afrika.
A ranar 6 ga wannan wata na Nuwamba ne Kungiyar kwallon Kwando ta Gombe Bull da Kwara Falcons suka shigar da Kara gaban babbar kotun tarayya dake Abuja inda suka bukaci kotun da ta dakatar da bangaren Musa Kida daga gudanar da gasar.