Labarai
NDLEA ta fitar da sunayen kasashe 8 da ta ke bukatar su bada biza ga masu son zuwa kasashen
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana sunayen wasu kasashe takwas da ta ke bukatar su ba da izinin biza ga wadanda ke da niyyar zuwa kasashen.
Kasashen sun hadar da: Thailand da Malaysia da Indonesia sai India da kuma Brazil da Philippines sai kasar Rasha.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar ta NDLEA Mista Femi Babafemi ya fitar a jiya Laraba.
Sanarwar ta bayyana sunan kasashen don musanta zargin cewa tana gabatar da haraji ne ga matafiyan, tana mai cewa bukatar da aka gabatar daga kasashen takwas ba sabon abu bane domi kuwa an shafe tsawon shekaru 24 ana gudanarwa.
A cewar sanarwar wannan wani mataki ne da zai kara bai wa hukumar damar yakar masu safarar miyagun kwayoyi tsakanin kasashe.
You must be logged in to post a comment Login