Kiwon Lafiya
Hukumar NERC ta baiwa kamfanonin rarraba lantarki wa’adin kwanaki 120
Hukumar kula da harkokin Wutar Lantarki ta kasa NERC ta baiwa kamfanonin rarraba Lantarkin wato DISCOs guda 11 wa’adin kwanaki 120 domin aiki da sabuwar nau’rar Mita da aka kirkiro don rage gibin da ake samu na matsalar wutar a kasar nan.
Tun a shekarar 2016 hukumar ta NERC ta sanar da cewa daga abokan huldar kamfanonin miliyan 7 da dubu 47, kusan miliyan uku suna da sabuwar Mitar, wanda hakan ya nuna cewa kusan miliyan 5 ba su da ita.
Domin cike gibin ne dai hukumar ta bullo da wani sabon tsari kan yadda jama’a za su iya mallakar Mitar cikin sauki amma ba a samu biyan bukata ba kasancewar lokacin da ake dauka kafin samar da ita.
Mai Magana da yawun hukumar ta NERC Usman Arabi ya ce aiki da sabuwar Mitar zai kawo karshen yadda ake shaci fadi wajen biyan kudin wuta ga wadanda ba su da mita da ma sauran matsaloli nan da shekaru uku masu zuwa.