Kiwon Lafiya
Hukumar NYSC zata bude sansanin rukunin C a jihar Gombe ga Yan jihohin Borno da Yobe
Hukumar dake kula da masu yi wa kasa hidima ta kasa NYC ta ce zata bude sansanin karbar horo na rukunin C na bana a jihar Gombe wanda aka sauya musu sansanin karbar horo daga jihohin Borno da Yobe.
Babban jami’in dake kula da shirin yi wa kasa hidima na jihar ta Borno Mr David Markson ne ya sanar da hakan a yau Litinin cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun Ms jami’ar hlulda jama’a a jihar Gombe Margaret Dakama.
Ms David Markson ya ce hukumar ta NYC ta amince da sauya masu yiwa kasa hidama dubu 1700 da suka hada da ‘yan jihar Gobe su dari 900 yayin da ‘yan jihar Borno su 400 sai kuma ‘yan jihar Yobe su 400, sansanin karbar horo.
A cewar sa duk dan yi wa kasa hidamar da abun ya shafa da yaje sansanin wucin gadi akan lokaci dake kwalejin kimiyya da fasaha ta Amada mai nisan kilomita 21 daga kan hanyar Bauchi zuwa Gombe a ranar Alhamis 5 ga wannan watan da muke ciki.
Akan haka ne babban jami’in ya gargadi masu yi wa kasa hidamar da su je sanssanin a kan lokaci don fara yin rijista da wuri da kuma tantancewa ganin za’a rufe shiga sansanin a daren ranar Lahadi 18 ga wannan watan