Kiwon Lafiya
hukumar rabon arziki ta kasa za ta fara bincikar bankuna game da haraji
Hukumar rabon arzikin kasa (RMAFC), ta ce nan gaba kadan ba da dadewa ba, za ta fara bincikar bankuna game da harajin da ake karba akan hada hadar kudi.
A cewar hukumar ta na tsammani za ta kwato sama da naira biliyan dari wadanda kudade ne, na haraji da ya kamata ya shiga asusun tarayya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Ibrahim Muhammed ya fitar jiya Lahadi, a Abuja.
Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan ranar da za a fara binciken ba.
Ibrahim Muhammed ta cikin sanarwar ya kuma ce, binciken na kwakwaf zai shafi kudaden haraji na hada-hadar kudi da wasu bankuna ashirin da biyu suka karba daga shekarar dubu biyu zuwa dubu biyu da goma sha takwas.
Sanarwar ta kara da cewa, bankunan kasuwancin kasar nan suna ciran ladar naira hamsin a duk ajiya da abokin huldar su yayi a asusun ajiyar sa da ya kai naira dubu daya ko sama da haka, kuma hakan na wakana tun a shekarar dubu biyu.