Labarai
Hukumar Taimakekiniya lafiya ta musanta zargin da ake yadawa
Hukumar kula da Asusun taimakekeniyar lafiya ta Jihar Kano ta musanta zargin da ake yi wa hukumar na cewa ba ko wace irin rashin lafiya hukumar ke kulawa da ita ba a cikin tsarin na taimakekeniyar lafiya.
Mataimakin daraktan hukumar Dr. Abdullahi Sa’ad Ahmad ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Mu Leka Mu Gano na nan gidan Radio Freedom, da aka gabatar a daren jiya wanda ya mayar da hankali kan batun taimakekeniyar lafiya da gwamnatin Jihar Kano ta bijiro da shi.
Dr. Abdullahi Sa’ad ya kara da cewa duk wani nau’i na rashin lafiya da mutum ke fama da shi yana karkashin tsarin taimakekeniyar lafiya na Kano, kuma ana ba su kulawa, bugu da kari kuma duk Asibitin da mutum ya zaba za a ba shi kulawar da ta dace.
Haka zalika Dr. Abdullahi Sa’ad ya nanata cewa sama da Asibitoci na gwamnati da kuma masu zaman kansu dari uku aka ware a nan Kano don kula da ma’aikatan Jihar Kano da ma sauran mutanen gari da suka yi rajistar tsarin, don duba lafiyarsu yadda ya kamata.
Gwamnatin Kano ta jadadda kudirin inganta kiwon lafiya
Fiye da ma’aikatan jihar Kano 3,000 ne su ka yi rijista da hukumar taimakekeniyar lafiya
An gurfanar da tsohon kwamishinan Lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf gaban babbar kotun Kano
Ya kuma kara da cewa ma’aikata su fahimci tsarin taimakekeniyar lafiyar da gwamnatin Kano ta bullo da shi, domin ko da ma’aikaci bai samu matsalar rashin lafiya ba kuma ana cire masa kudi ana tallafawa wasu ma’aikata ne da ke fama da matsalar rashin lafiya, kuma nan ba da jimawa ba za suwaiwayi ‘yan Fansho don sanya su a cikin tsarin.