Labaran Wasanni
Hukumar wasan motsa jiki ta duniya WA ta cire sunan Shehu Gusau daga shafinta
Hukumar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya WA, ta cire sunan Shehu Gusau daga shafinta na karfar Internet a matsayin shugaban hukumar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta Najeriya AFN.
Hukumar ta duniya ta dauki wannan matakin ne kwanaki kadan bayan kammala mabanbantan zabukan shugabancin hukumar AFN da ya rabu gida biyu kuma aka gudanar a ranar 14 ga watan Yuni inda Shehu Gusau da Tonobok Okowa kowanensu ke ikirarin zama zababben shugaban hukumar.
Haka zalika WA ta kuma goge sunan babban daraktan hukumar AFN Siminialayi Pepple daga shafin nata.
AFN ta kasance cikin rikici tun daga shekarar 2019 bayan da kwamitin gudanarwa da Gusau ke jagoranta ya bukaci ma’aikatar wasanni ta kasa ta baiwa hukumar damar cin gashin kai.
Hakan ne dai ya haifar da dakatar da Gusau tare da magoya bayansa daga shugabancin hukumar.
You must be logged in to post a comment Login