Labarai
Hukumar zabe ta dage cigaba da tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Nasarawa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dage cigaba da tattara sakamakon zabe na ‘yan takarar gwamnan da ake biyo bayan tada hargitsi a cibiyar tattara sakamakon zabe na karamar hukumar Nasarawa da misalin karfe daya da rabin dare na tsakar daran jiya.
Baturin zaben hukumar zabe dake nan Kno farfesa B.B Shehu tare da kwamishinan zabe na jihar Kano Farfesa Riskuwa Shehu suka sanar da hakan jim kadan bayan kama mataimakin Gwamnan jihar Kano Nasiri Yusuf Gawuna da kwamishinan kanann hukumomi Murtala Sulen Garo da kuma shugaban karamar hukumar Nasarawa Lamin Sani saboda zargin kai hari ofishin tattara sakamakon zabe bayan da suka jagiranci ‘yan bangar siyasa don tada hargitsi.
Farfesa B.B Shehu ya bukaci masu ruwa da tsaki a ofishin hukumar zaben cewa da su yi hakuri za’a dage cigaba da tattara zaben kasancewar akwai bukatar su shiga taron gaggauwa don tattauna batun, yayin da nan da dan lokaci za su dawo don kammala tattara sakamakon karamar hukumar ta Nassarawa.
Haka zalika jami’an ‘yan sanda sun tsare mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna da kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo da kuma shugaban karamar hukumar Nasarawa Lamin Sani a shalkwatar rundunar dake nan Kano.
Da yake ganawa da manema labarai a shalkwatar rundunar ‘yan sanda dake nan Kano jagoran jam’iyyar PDP dake nan Kano Rabiu Musa Kwankwaso wanda yake tare da magoya bayan sa ya bayyana takaicin sa kan zargin kama wadanda ake zargin da kawo hargitsi a yayin tattara sakamakon.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce bai dace a ce irin wadandan mutanan ne suka aikata hakan, su da ya kamata a ce suke wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma, amma kuma suka kawo tarnaki wajen cigaba da tattara sakamakon.
Wakilin mu Abudullateef Abubakar Jos ya so jin ta bakin jagoran jam’iyyar APC Abdullahi Abbas kan wannan batun ya ce ba zai ce komai, ganin bai san mai ake ciki ba.