Labarai
Hukumomi sun rufe asibitin Maita a Kano
Hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu ta jihar Kano da hadin gwiwar hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano sun rufe wani asibitin Maita da aka bude a nan Kano.
Asibitin wanda Chiroman sarkin mayun Kano, Alhaji Yahya Ali ya bude a garin Gano dake karamar hukumar Dawakin Kudu, ana kwantar da marasa lafiya tare da lura dasu ta hanyar maita.
Wasu majinyata da aka samu a asibitin sun bayyana cewa ana kafa musu kusa tare da zuko ruwa daga cikinsu da sunan yi musu magani.
Sai dai da farko wasu daga majinyatan sunyi kemadagas sunki yarda a dauke su daga asibitin mayun zuwa na gwamnati kamar yadda wakilinmu Aminu Abdu Bakanoma ya rawaito mana.
Kazalika a yayin da aka tura Chiroman Mayun zuwa kotu nan take ya fadi ya kuma marai-raice cikin halin rashin lafiya a harabar hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano.
Amma tuni jami’an hukumar sun garzaya da shi asibiti domin tabbatar da cewa shin rashin lafiya ce ta zahiri ko kuma kirkirarriya ce.
Idan zaku iya tunawa dai tun a watannin baya ne dai hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta cafke tawagar sarkin mayun jihar Kano da wasu daga ‘yan majalisarsa wanda cikin binciken da ake musu ya kai ga bankado wannan asibiti.
Labarai masu alaka:
Sarkin mayun boge ya karyata kansa
Mun kama Sarkin mayu na bogi-Muhiyi Magaji