Connect with us

Ƙetare

Hukumomin Amurka sun tabbatar da mutuwar fiye da mutane 100 a ambaliyar Texas

Published

on

Hukumomi a jihar Texas da ke Amurka sun bayyana cewa adadin waɗan da suka mutu sakamakon ambaliyar Ruwa  jihar sun zarta 100.

 

Masu aikin ceto na ci gaba da lalubo gawarwaki, yayin da da kawo yanzu ba a iya tantance adadin waɗanda suka ɓace ba.

 

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata mummunar ambaliya ta auka wa jihar sakamakon mamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske haɗe tsawa.

 

Masu gudanar da wani wurin shaƙatawa, da ambaliyar ta rasa – sun tabbatar da mutuwar ƴan mata 27 da ke wurin a lokacin da ambaliyar ta ratsa yankin.

 

Al’umma na ganin rashin ware isassun kuɗi wa ɓangaren kula da yanayi a kasafin kudin ƙasar ne ya haifar da matsalar, zargin da gwamnatin Amurka ta musanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!