Labaran Wasanni
IAAF: An tura tsohon shugaban hukumar gidan gyaran hali
Tsohon shugaban hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya wato IAAF, Lamine Diack, an yanke masa hukuncin dauri a gidan gyaran hali sakamakon samun sa da hannu a aikata cin hanci da rashawa.
An dai zargi shugaban mai shekaru 87, da badakalar kudaden da suka shafi ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar Rasha.
Lamine Diack dan kasar Senegal, ya karbi kudade daga hannun ‘yan wasan kasar ta Rasha don yin rufa-rufa, sakamakon samun su da laifin amfani da kwayoyin kara kuzari da kuma kyale su ci gaba da wasanni Olympics na shekarar 2012 da aka gudanar a birnin London.
Mahukuntan kasar Faransa da suka gudanar da bincike akan zargin ne, suka yanke wa tsohon shugaban hukuncin daurin shekara 4 a gidan gyaran hali tare da biyan tarar Yuro 500,000.
Haka zalika, lauyan dake kare tsohon shugaban ya ce basu gamsu da wannan hukuncin ba, yana mai cewa za su daukaka kara zuwa kotu ta gaba.
You must be logged in to post a comment Login