Labaran Kano
Ilimi shine ginshikin cigaban rayuwa -Dagacin Bechi
Dagacin garin Bechi ta, karamar hukumar Kumbotso Alhaji Lawan Yakubu Bechi, ya bayyana ilimi a matsayin abinda ke da muhimmanci tare da taka gagarumar rawa, wajen cigaban al’umma.
Dagacin ya yi kiran ne a wajen saukar karatun Al’qur’ani mai girma na makarantar Hubbin Nabiyyi (SAW) dake garin Bechi karo na farko da dalibai goma sha uku su kayi.
Alhaji Lawan Yakubu Bechi, ya ce ilimi ne kadai ke bada damar samun cigaban da ake muradi a rayuwa.
Dagacin garin Kantama yayi Murabus
Bawa mata ilimi na da muhimmanci sakamakon yawansu- Farfesa Aliyu Musa
Da yake jawabi, dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Kumbotso a wajen saukar Mudassir Ibrahim Zawachiki, ya bukaci iyayen yara dasu kara sanya idanu wajen ganin ya’yansu sun samu ilimi mai nagarta.
Shamsu Dau Abdullahi, wakilin mu da ya halarci taron ya rawaito cewa daliban da suka sukayi haddar ta sauka, akwai masu wadanda suke da izifi talatin -talatin da kuma goma goma.
You must be logged in to post a comment Login