Labarai
IMF ta shawarci CBN da ya kara wa’adin daina amfani da tsohon kudi
Bankin bada lamuni na duniya IMF ya shawarci babban bankin Najeriya na CBN da ya kara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudi daga ranar 10 ga watan da muke ciki na Fabrairu, sakamakon irin wahalar da yan Najeriya ke sha wajen neman sabbin kudin.
Babban jami’in bankin IMF a Najeriya Ari Aisen ne ya bukaci hakan a yau Laraba cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce, wa’adin karin kwanakin 10 da babban bankin kasa CBN ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun kudin yayi kadan, a don haka akwai bukatar sake sanya wani sabon wa’adin.
A cewarsa, ‘duk da karin wa’adin, har yanzu yan Najeriya na shan wahala wajen samun sabbin takardun kudin maimakon su samu cikin sauki, har ma ya nuna fargaba kan yadda matsalolin da ake fuskanta ka iya haifar da zanga-zanga da tashe-tashen hankula a fadin kasar nan.’
Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login