Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ina nan a jam’iyyar APC – Murtala Sule Garo

Published

on

Ɗan takarar mataimakin Gwamna a jam’iyyar APC Alhaji Murtala Sule Garo ya musanta rahoton cewa ya fice daga jam’iyyar APC.

Murtala Garo ya shaida wa Freedom Radio cewa, yana nan daram a cikin jam’iyyar APC bai sauya sheƙa ba.

Ya ce “Ƙarya ne, ni yanzu ma (ƙarfe biyu na daren Talata) meeting muke yi da Gwamna, ƙarya ce kawai mutane suke yaɗawa”.

Wannan dai ya biyo bayan rahotonnin da aka riƙa yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP a kafafen sada zumunta.

Murtala Garo wanda shi ne tsohon Kwamishinan ƙananan hukumomi na Kano, na cikin ƴan gabada-gabadai ɗin Gwamna Ganduje.

A baya dai Murtalan ya ajiye muƙaminsa ne domin yin takarar Gwamna, kafin daga bisani jam’iyyar tayi maslaha inda ta tsayar da mataimakin Gwaman mai ci Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, tare da Murtalan a matsayin mataimaki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!