Kaduna
Inconclusive: Kotu ta umarci a sake zaɓe a jihar Kaduna
Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe da ke zamanta a Kaduna, ta bayyana zaben gwamnan jihar na 2023 a matsayin wanda bai kammala ba.
Kotun ta yi hukunci ne a zamanta na ranar Alhamis inda ta bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba tare da bayar da umarnin sake gudanar da wani zaɓen ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC cikin kwanaki 90.
Tawagar alƙalan su uku ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Victor Oviawe, ya bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe a rumfunan zabe 24 da ke gundumomi bakwai na ƙananan hukumomi huɗu da suka kunshi masu rajista 16,300.
Zaman yanke hukuncin dai ya gudana ta kafar Zoom, bayan alkalan sun kaurace wa zauren taron.
Idan za a iya tunawa jam’iyyar PDP da dan takararta Isah Mohammed Ashiru ne suka shigar da ƙarar, suna ƙalubalantar nasarar Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC bisa zargin maguɗin zaɓe.
You must be logged in to post a comment Login