Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Independence day: Jaruman Kannywood da na TikTok sun sauya salon bikin ranar ƴancin kai

Published

on

Jaruman masana’antar Kannywood da na TikTok sun ƙauracewa murnar bikin ranar samun ƴancin kan Najeriya.

A kowacce shekara dai ana ganin yadda jaruman ke sanya riguna mai kalar Fari da Kore tare da yin shagulgula don murnar ranar.

A wani ɓangare ma matasan kan shafe jikinsu da fenti kalar Fari da Kore tare da riƙe tutoci mai nuna alamar Najeriya.

Sai dai a bana bikin ya sauya salo domin kuwa an hango jaruman ɗauke da kwalaye mai rubutu da ke nuna alamun “Najeriya na buƙatar fita.”

Haka kuma wasu kwalayen na ɗauke da rubutun cewa “a daina garkuwa da mu, a sako mana yaransu.”

Wasu kwalayen na ɗauke da cewa “a samar mana ayyukan yi, a yi mana maganin matsalolin tsaro.”

Wannan salo na bana dai na zuwa ne yayin da Najeriyar ke fama da ƙalubale na rashin aikin yi, garkuwa da mutane, harin ƴan bindiga matsin tattalin arziki, da dai sauransu.

Haka kuma salon jaruman ya ja hankalin al’umma da dama, domin kuwa ana ganin cewa kamata ya yi matasa su zamo masu murya ɗaya da haɗin kai ta fannin abubuwan da suke damun ƙasa.

Bikin samun ƴancin kan daga turawan mulkin mallaka na zuwa ne karo na 63.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!