Connect with us

Labarai

Shugaban INEC ya bayyana damuwa kan ta’azzarar matsalar tsaro

Published

on

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana damuwa matuka kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a sassan kasar nan, yana mai gargadin cewa hakan na iya zama babban barazana ga gudanar da zabuka masu inganci, gaskiya da adalci a kasar.

Farfesan ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya hada manyan masu ruwa da tsaki a harkar zabe, inda ya jaddada cewa rashin tsaro na hana jami’an zabe gudanar da aikinsu yadda ya kamata, tare da kawo cikas ga masu kada kuri’a wajen fitowa domin zaben shugabanninsu.

Ya ce a wasu yankuna, matsalolin kamar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da kuma rikice-rikicen kabilanci na sanya jama’a cikin tsoro, lamarin da ke rage yawan masu kada kuri’a, tare da iya haifar da rashin sahihancin sakamakon zabe.

Farfesa Amupitan ya kara da cewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba domin magance matsalar tsaro, hakan na iya janyo koma baya ga dimokuradiyya a Najeriya, musamman a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da muhimman zabuka nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!