Connect with us

Labarai

Atiku ya yi gargadi kan yunkurin dakatar da yakin neman zabe a wasu sassan Arewa

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Alhaji  Atiku Abubakar, ya yi gargadi kan yunkurin dakatar da yakin neman zabe a wasu sassan Arewacin Najeriya da ya ce hakan na iya tauye hakkin kundin tsarin mulki da kuma kara fargabar hana jama’a damar kada kuri’a a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara tsananta.

Martanin Atiku ya biyo bayan rahotannin da ke cewa majalisar dattawa na nazarin yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a jihohi takwas da ke fama da karuwar tashe-tashen hankula, a arewacin kasar nan.

Atiku ya ce lamarin abin damuwa ne matuka, yana mai cewa duk da cewa rashin tsaro babbar matsala ce, bai kamata a yi amfani da ita wajen takaita shiga harkokin dimokuradiyya ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa al’ummar Arewa, kamar sauran ‘yan Najeriya, suna da hakkin samun tsaro da kuma cikakkiyar damar shiga harkokin dimokuradiyya.

Madugun adawar ya ce  alhakin gwamnati ne ta tabbatar da tsaro, kamar yadda ya kamata a bar ‘yan kasa su yi amfani da hakkokinsu na kasa ba tare da tsoro ko tsangwama ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!