Labarai
INEC ta samar da sabon tsarin yin rajistar katin zabe ta Internet
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ce za a yi aikin rajistar samar da katin zabe ta Internet a wasu cibiyoyin samar da katin, a kokarin magance matsalolin cinkoson masu jefa kuri’a a cibiyoyi daban-daban a Najeriya.
A cewar hukumar ta INEC sabon shirin zai yi tasiri wajen rage cunkoson a cibiyoyin yin rajistar.
Kwamishinan yada labarai da ilimantar da masu jefa kuri’a na hukumar, Festus Okoye ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da jaridar Punch a jiya Litinin 22 ga watan Maris din 2021.
Yace, sabon tsarin zai bada damar yin rijistar ta Internet ba sai mutum yaje cibiyoyin ba wannan hakan zai zo ne gabanin zaben shekarar 2023.
Idan za a iya tunawa dai hukumar INEC tun a watan Nuwamba na shekarar 2020 ta yi alkawarin cewa za ta ci gaba da rijistar masu kada kuri’a, wanda aka dakatar tun a watan Agustan 2018, inda tayi alkawarin ci gaba da yi a zangon farko na shekarar 2021.
You must be logged in to post a comment Login