Labarai
Yanzu yanzu: INEC ta sanya ranar zaben shekarar 2023
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanya ranar 18 ga watan Fabarairun shekarar 2023 a matsayin ranar da za a gudanar da babban zaben kasa.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da hakan yau, lokacin da yake jawabi a gaban kwamitin majalisar dattijai kan hukumar INEC, kan yadda za a samar da hukumar kula da laifuffukan da aka aikata lokacin zabe.
Farfesa Mahmud Yakubu ya ce bayan shafe tsawon shekaru 13 ana tattaunawa kan shawarwarin da Justice Muhammad Uwais ya bayar don samar da hukumar kula da laifukan zaben, yanzu haka dai sun kawo wannan gaba.
Ya kara da cewa a zaben shekarar 2015, sun karbi korafe-korafe 124 inda ya zuwa yanzu aka zartar da hukunci a kan guda 60.
Tun da fari shugaban kwamitin majalisar dattijan Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya ba da tabbacin cewa kudurin dokar zai samu sahalewar shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan sun kammala amincewa da shi.
You must be logged in to post a comment Login