Addini
Inyass ya tabbatar wa Muhammadu Sanusi na 2 jagoranci Ɗarikar Tijjaniya a Najeriya
Jagoran ɗarikar Tijjaniya na duniya Sheikh Muhammadul Mahi Inyass, ya tabbatar wa Sarkin Kano na goma sha hudu a daular fulani, Malam Muhammadu Sanusi na biyu mukamin jagoran ɗarikar Tijjaniya a Najeriya.
Mai magana da yawun tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN) Sa’adatu Baba Ahmad ce ta sanar da hakan ta cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na facebook a yau litinin.
Ta ce shugaban ɗarikar Tijjaniya ta duniyar ya tabbatar wa Malam Muhammadu Sanusi na biyu jagoranin Tijjaniyar ce a garin Madina Baye Kaulaha da ke kasar Senegal, bayan kammala sallar asham a jiya lahadi.
Tun bayan rasuwar tsohon jagoran ɗarikar marigayi Sheikh Khalifa Isyaku Rabi’u a shekarar 2018, ɗarikar ta Tijjaniya ba ta nada sabon shugaba ba.
Idan za a iya tunawa ko da kakan sarkin na goma sha hudu wato Muhammadu Sanusi na daya ya rike mukamin na jagoran ɗarikar Tijjaniya
You must be logged in to post a comment Login