Labarai
Rashin tsaro da lalacewar hanya ne ke haddasa wahalar mai a Nigeriya-IPMAN
Kungiyar IPMAN ta alakanta rashin kyan hanya, da kuma karancin tsaro a matsayin abinda yake haddasa wahalar man da ake fama dashi a Arewacin kasar nan.
shugaban kungiyar dillalan man fetur ta kasa reshen Jihar Kano IPMAN Alhaji Bashir dan Malam ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da Freedom Radio.
Bashir Dan Malam ya ce da hanyar da motocin da suke dauko man daga Kudu zuwa Arewa basu lalace ba, motocin dakon man baza su rinka shan wahala kafin kawo man ba.
Wanda yace rashin cikakken tsaro ma akan hanyar na taka rawa wajen hana motocin nasu zirga-zirga da daddare.
Yana mai cewa wannan matsalar suma tana damunsu, don haka kungiyar ke kira da DSS din dasu sanya baki wajen gyara hanyar, da samar da tsaro. tare kuma da bawa ‘yan kasuwa dala, don shawo kan wannan matsalar.
You must be logged in to post a comment Login